![]() |
Akpabio/Natasha |
Sanata mai wakiltar Ekiti ta Kudu kuma shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Yemi Adaramodu, ya ce abin da Natasha ta yi a majalisar dattawa ba shi da maraba da wasan kwaikwayo.
Adaramodu ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels TV a cikin shirin Politics Today a ranar Laraba.
Sanatan ya ce kwamitin majalisar dattawa kan da’a ya fara duba akan koke-koken Natsaha ta shigar kan shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio.
Daily Trust ta ruwaito cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta kai koke gaban majalisar dattawa kan zargin yin lalata ake yi wa Akpabio,a cikin hirar sanata Adaramodu ya bayyana hakan a matsayin wasan kwaikwayo.