Gwamnatin jihar Anambra ta gargadi masu wa’azi da su guji kure lasifika a bainar jama’a, musamman wuraren taruwar jama'a da hayaniyar ke damun su.
Gwamnan jihar Chukwuma Soludo, ya bayyana cewa duk wanda aka kama da karya wannan dokar za a ci shi tarar Naira 500,000.
Daga karshe ya shawarci limaman coci masu wa’azin da su dinga yin wa'azuzukan su a cikin coci da masu son saurara zasu iya ji a harabar Cocin.
Category
Labarai