Kamfanin samar da lantarki na Nijeriya ya bayyana cewa wutar lantarkin da ake samu a kasar ta karu zuwa megawatt 5,713.60, kari mafi yawa da aka samu cikin shekaru hudu da suka gabata.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, TCN ta sanar da cewa, bangaren samar da wutar lantarki ya kafa wani tarihi a shekarar 2025.
Ya bayyana cewa zuwa ranar Talata 14 ga watan Fabrairu, yawan lantarkin da ake samar wa ya zarce 5.543MW.