An jiyo wasu manya-manyan jiga-jigan jam’iyyar APC sun fara yakin neman zaben shugaba Tinubu karo na biyu na zaɓen a 2027
Jiga-jigan sun hada da shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Ganduje da sakataren gwamnatin tarayya George Akume, sun yi kira ga shugaba Tinubu da ya sake tsayawa takara a karo na biyu.
A kwanakin baya dai shugaban jam'iyyar na kasa Abdullahi Ganduje ya bukaci ‘yan siyasar Arewa da suyi hakuri a zaben 2027 su bai wa shugaba Tinubu ya ida wa’adinsa na biyu.
Shima sakataren gwamnatin tarayya George Akume, yayin da yake magana a wani shirin gidan talabijin na TVC, ya shawarci ’yan Arewa da kada su nemi kujerar shugaban kasa a 2027 su bari sai shekarar 2031.
Category
Labarai