Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i ya fice daga jam'iyyar APC ya kuma SDP


Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ya koma jam’iyyar SDP.

Tsohon gwamnan ya bayyana ficewar sa a shafinsa na Facebook yana mai cewa "daga yau 10 ga Maris na shekarar 2025 na fice daga jam’iyyar APC".

Nasir El-Rufai ya bayyana cewa a shekara biyun da jam’iyyar APC ta yi babu wani abin a zo a gani da ta aiwatar ga 'yan kasa.

Tsohon gwamnan ya jaddada cewa zamansa na shekaru takwas a matsayin gwamnan jihar Kaduna ya samar da ci gaba a fannin ilimi da kiwon lafiya da ababen more rayuwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp