Wani babban taro da limaman ɗarikar Katolika suka gudanar a Nijeriya ya bayyana cewar tsare-tsare da manufofin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu sun jefa miliyoyin ƴan kasar cikin ƙangin talauci.
Babban jagora kuma limami a đarikar Bishop Lucius Iwejuru Ugorji, ya ce manufofin gwamnati sun haifar tsadar rayuwa sakamakon hauhawan farashin kayan masarufi, abinda ya sanya jama'a da dama cikin talauci.
Ugorji ya ce sauye-sauyen da gwamnatin ta zo da su, sun sanya tashin farashin kayayyakin masarufi sakamakon janye tallafin man fetur inda aka ci gaba da samun tsadar sufuri da kuma kayayyakin da ake buƙata na yau da kullum.