Tinubu ya yi watsi da kasafin kudin kidaya na N942bn


Shugaba Tinubu ya yi watsi da kudirin hukumar kidaya a Nijeriya da ta gabatar na Naira biliyan 942 wanda zata gudanar da aikin kidayar gidaje da na jama’a a fadin kasar.

Jaridar Punch ta rawaito wata majiya mai tushe ta ce an tattauna tsakanin shugaba Tinubu da manyan jami’an hukumar a ranar Litinin, 24 ga watan Fabrairu na 2025, ta bayyana cewa Tinubu ya bukaci da a rage yawan kudaden tare da sanyo da matasa masu yi wa kasa hidima domin su gudanar da aikin.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp