![]() |
Christopher Musa |
Hedkwatar tsaron Nijeriya ta sanar da cewa sojoji sun halaka 'yan bindiga 92, tare da kama wasu 111, yayin da aka kubutar da mutane 75 da aka yi garkuwa da su, duk a cikin makon da ya gabata.
Daraktan yada labarai na hedkwatar tsaron, Maj.-Gen. Markus Kangye, ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai ranar Alhamis a Abuja.
Markus Kangye ya bayyana cewa sojojin sun kuma kwato makamai iri-iri da suka kai 117 da alburusai 2,939.
Kangye ya bayyana cewa, sojojin sun kuma kama wasu mutane 18 da ake zargi da hannu wajen satar danyen, haka kuma sun yi nasarar dakile ayyukan satar mai da kudinshi ya kai naira miliyan 521.8 a yankin Kudu maso Kudu.