Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga 'yan kasar su dage da yin addu'a ga shugabanni da neman zaman lafiya da a cikin watan Ramadan

Bola Ahmad Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga 'yan kasar su dage da yin addu'a ga shugabanni da neman zaman lafiya da a cikin watan Ramadan

Da yake jawabi a ranar Litinin a masallacin fadar shugaban kasa yayin bude Tafseer na watan Ramadan, shugaban wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Kashim Shettima, ya bukaci ‘yan Nijeriya da su rungumi dabi’ar zaman lafiya, da kyautatawa, da adalci a tsakaninsu.

Shugaba Tinubu ya karfafa gwiwar ‘yan kasar da su inganta alakarsu da abokan zamansu, tare da yin watsi abinda da zak raba kan al’umma.

Ya kuma tunatar da su muhimmancin hadin kan al'ummar kasa da kuma hadin gwiwa wajen tunkarar kalubalen kasar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp