![]() |
Janar Abdulrahman Tiani |
Shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya jagorancin bikin daga sabuwar tutar kungiyar kasashen AES a hukumance wanda ya gudana a Jamhuriyar Nijar.
Shugaba Tiani ya jagoranci wannan biki ne a fadarsa da ke a babban birnin Yamai a gaban membobin gwamnatinsa.
A makonnin da suka gabata ne shugaban kungiyar AES kuma shugaban kasar Mali Janar Assimi Goïta ya gabatar da sabuwar tutar kungiyar ga ministocin kasashen uku da suka halarci wani taro a birnin Bamako.