Tsohon Sanatan jihar Kaduna Shehu Sani ya ce Gwamnan Kaduna Uba Sani ne ya yi sanadiya komawar sa jam’iyyar APC, bayan wani zaman sulhu a jihar.
Dan gwagwarmayar ya tabbatar da cewa yana cikin wadanda suka kafa jam’iyyar APC a jihar Kaduna kuma ya bayar da gudunmawa wajen dora jam’iyyar a kan turba.
Da yake zantawa da gidan talabijin na Channels, Shehu Sani ya kuma bayyana cewa takun-saka da ta shiga tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ita ce ta yi sanadin fitar sa jam'iyyar a baya.
Category
Labarai