![]() |
Shehu Sani |
Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana cewa da kyar ya tsallake rijiya, bayan da majalisar dattawa ta yi yunkurin dakatar da shi a shekarar 2018 saboda ya bayyana albashi da alawus-alawus na ‘yan majalisar Dattawa.
A cewar Shehu Sani, ba don shugaban majalisar dattawa na lokacin Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ekweremadu sun sanya baki ba, shima da an dakatar da shi na tsawon watanni shida.
Ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X bayan dakatar da Sanatar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan.
Jaridar Punch ta rawaito Shehu Sani na cewa, muddin mutum yana cikin majalisa kuma ya fallasa wani abu to babu wani Sanata da zai goyi da bayansa.