Nasiru Abdullahi Mai Kano, makusancin Malam Nasir El-Rufai ya zama shugaban riko na jam’iyyar SDP a jihar Kaduna

 

An nada wani na hannun damar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a matsayin shugaban riko na jam’iyyar SDP a jihar Kaduna.   

Nasiru Abdullahi Mai Kano, dan siyasa ne, ya taba zama dan majalisar dokokin jihar Kaduna, mai wakiltar mazabar Unguwar Sanusi na tsawon shekaru.

Daily Trust ta rawaito cewa shugabannin kwamitin rikon kwaryar za su yi aiki na tsawon watanni uku, kafin babban zaben shugabannin jam'iyyar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp