Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ya jaddada kudirin gwamnatin tarayya na samar da lantarki mai ɗorewa ga ‘yan Nijeriya

 

Adebayo Adelabu

Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ya jaddada kudirin gwamnatin tarayya samar da ingantacciyar wutar lantarki ga ‘yan Nijeriya.

Mai bai wa ministan shawara na musamman kan harkokin sadarwa Bolaji Tunji ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Laraba.

A cewarsa irin nasarorin da aka samu a bangaren samar da wutar lantarkin, ya nuna kudurin da gwamnatin tarayya ke da shi na kawo gyara.

Ya ce, bangaren ya samu nasarorin da ba a taba ganin irinsa ba a fannin samar da wutar lantarki kuma wannan babbar nasara ce ga Nijeriya.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp