Matasa masu yi wa kasa hidima sun nuna rashin jin dadinsu da kasa aiwatar da biyan sabun alawus na naira 77,000 ga matasan.
Tun a watan Yulin 2024 ne gwamnatin ta amince da kara kudin na alawus daga naira 33,000 zuwa 77,000, Hakama darakta janar na hukumar ta NYSC Brig. Gen. Yushau Ahmed ya tabbatar da cewa za a fara biyan kudin a watan Fabrairun 2025.
Sai dai jaridar Punch ta ruwaito cewa har yanzu ba a fara biyan sabon alawus din ba, kamar yadda wasu matasan suka bayyana cewa naira N33,000 suka karba a matsayin alawus a watan na Fabrairu.
Category
Labarai