Masu garkuwa da mutane sun yi shigar jami'an EFCC tare da yin awon gaba da mutum 10 a Neja


Wasu ‘yan bindiga da sojan gonar jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Nijeriya EFCC, sun yi garkuwa da mutane 10 a wani otal da ke kan hanyar Shiroro a karamar hukumar Chanchaga a Jihar Neja.

Wani mai lura da harkokin tsaro Zagazola Makama, ya ruwaito wata majiya na cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:58 na safiyar ranar Talata, 27 ga Fabrairu, 2025.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki otal din ne, inda suka yi ikirarin cewa jami’an hukumar EFCC ne.


 

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp