Mai zuwa ibada coci ya sace limamin cocin a Adamawa


Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta yi nasarar kubutar da wasu limaman cocin Katolika guda biyu da aka yi garkuwa da su a wani samame na hadin gwiwa da suka kai a maboyar ‘yan ta’adda a jihar.

A cewar wata sanarwa da kakakin rundunar SP Suleiman Yahaya Nguroje ya fitar ya ce an kubutar da limaman cocin ne a kauyen Gwaida Malam da ke da iyaka da kananan hukumomin Numan da Demsa.

An dai zargi Tahamado Jonathan Demian mai shekaru 34 da yin garkuwa da Abraham Samman na Cocin Katolika na Yola da Matthew David Dusami na Cocin Katolika na Jalingo.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp