Lauya ya maka alkali kotu yana neman diyyar Naira milyan 610 a jihar Nasarawa

Wani lauya, mai suna Isah Hassan Nalaraba, ya shigar da kara, inda yake zargin an ci zarafinsa, da yake neman a biya shi diyyar kudi Naira milyan 610, a kan wani alkalin Babbar Kotun Jihar Nasarawa, mai suna Abdullahi Hassan Shama.

Lauyan ya shigar da karar, inda yake zargin an tsare shi ba bisa ka’ida ba da tilasta kwace wayoyinsa na hannu kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta rawaito.

Lauyan ya shigar da karar a ranar 7 ga watan Fabrairu a babbar kotun tarayya da ke Lafia, babban birnin jihar Nasarawa a takardar kara mai lamba FH/LF/FHR/6/2025, inda ake zargin Shams da cin zarafinsa yayin da ya bayyana a gaban babbar kotun Doma a ranar 5 ga Fabrairu, 2025.

Waɗanda ake karar su ne mai Shari'a Abdullahi Hassan Shams, rajistaran babbar kotun Doma, kwamishinan 'yan sanda, rundunar 'yan sandan Nijeriya, da Dahiru Maruf, wanda 'orderly' ne.

A cikin wata takardar 'affidavit' da aka hade da jarar, mai ɗauke da kwanan wata 11 ga Fabrairu, Nalaraba ya bayyana cewa ya gabatar da wata bukata ga kotu yana neman alkalin ya janye kansa daga sauraren shari'ar saboda yuwuwar nuna son zuciya.

Amma alkalin ya ki, yana jaddada cewa zai saurari duka bukatar janyewa da kuma ainihin shari’ar.

A cewarsa, wannan ya sa ya sanar da ficewarsa daga shari’ar.

Nalaraba ya bayyana matakan alkalin a matsayin wanda bai dace da kundin tsarin mulki ba kuma sun take masa hakki karkashin sassan doka na 34, 35, 36, 37, da 41 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999.

Saboda haka, ya nemi kotun ta ayyana cewa kama shi, tsare shi, da kwace wayoyinsa ba bisa doka ba ne kuma an take hakkinsa.

Lauyan ya kuma nemi umarnin kotu da ya tilasta wa wadanda ake kara su biya kudi Naira miliyan 200 a matsayin diyya saboda kwace wayoyinsa da kuma hana shi kokarin isar da sako da wayoyinsa.

Kazalika, lauyan ya nemi wadanda ake kara su biya Naira miliyan 150, a matsayin diyya ta musamman saboda kama shi ba bisa ka’ida ba, tsare shi, da kuma kwace wayoyinsa na GSM da kuma cin zarafin da aka yi masa karkashin Sassan 34 [1], 35 [3], 2 [6], 36 [1], 37, 41 [1], da 44 [1] na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999.

Haka kuma akwai diyya ta Naira miliyan 10, a kan wadanda ake kara da mai shigar da karar ya nema.

Tun da farko, a cikin wata takardar korafi wato 'pettition' da ya aika wa shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa NBA, Afam Asigwe, lauyan ya zargi alkalin da kwace wayoyinsa da kuma ba da umarnin tsare shi.

An dai dage shari'ar zuwa ranar 29 ga Afrilu, 2025.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp