![]() |
Lamine Yamal |
Dan wasan Barcelona Lamine Yamal zai sanya hannu a sabon kwantiragi da kungiyar tasa kamar yadda wakilinsa Jorge Mendes ya bayyana.
Mendes ya ce sunyi magana da Lamine bayan wata ganawa da suka yi da jami'an kungiyar Barcelona a Lisbon.
Sabon kwantiragin da ake kyautata zaton zai dauki dogon lokaci, na zuwa ne a daidai lokacin da dan wasan ya cika shekaru 18.