![]() |
Nasir Idris |
A wani harin ramuwar gayya kan halaka shugaban Lakurawa Maigemu, da hadin gwiwar jami’an tsaro suka yi a ranar Alhamis din da ta gabata, a ranar Lahadin karshen mako kungiyar Lakurawa ta kai hari a yankin Birnin Dede da ke karamar hukumar Arewa ta jihar Kebbi da suka halaka mutane 13.
Kungiyar wadda ta kunshi mutane daga kabilu daban-daban da suka hada da Hausawa, Fulani, Toureg, Barebari da sauran kabilu, ta dade tana aikata ta'addanci a jihar Kebbi da kewaye.
Wani dan yankin jihar Kebbi, Musa Gado, ya ce ‘yan ta’addan sun kuma kona kauyuka takwas da ke yankin a yayin harin, da ya ce, maharan sun bar wani kauye daya kacal da sojoji ke gadi.
Wani dan yankin mai suna Suleiman Abubakar, wanda ya ce ya rasa dan uwan sa a harin, ya shaida wa Daily Trust cewa, ‘yan ta’addan sun mamaye al’ummar yankin ne da daddare, bayan kammala sallar magrib.
Sauran kauyukan da maharan suka kona sun hada da; Birni Garin Nagoro, Yar Goru, Dan Marke, da Tambo.