Kwamitin da'a na majalisar dattawa ya bayar da shawarar dakatar da Sanata Natasha na watanni 6

Akpabio/Natasha

Kwamitin da’a na Majalisar Dattawa ya ba da shawarar a dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan sakamakon zargin yin lalata da ta yi wa shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.

Kwamitin ya kuma ba da shawarar cewa dole ne Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya ya nemi gafarar majalisar dattawa saboda rashin girmamawa ga majalisar.

A tsawon lokacin dakatarwar, kwamitin ya bayyana cewa za a rike mata albashi tare da janye mata jami'an tsaro.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa ana ci gaba da muhawara kafin daukar matakin ladabtarwa kan Natasha.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp