Kotun Gabon ta yi watsi da takardun takara 19

  


Takardun 'yan takarar shugaban kasa a Gabon hudu ne kotun tsarin mulkin kasar ta amince da su cikin 23 da suka ajiye takardun nuna bukatar yin takarar shugaban kasar a zabe mai zuwa na ranar 12 ga watan Aprilun nan mai kamawa 

Kotun ta ce wadanda aka yi watsi da takardun nasu suna da sa'o'i 72 domin daukaka kara a gaban kotu 

Cikin wadanda kuma aka yi watsi da takardun nasu har da fitaccen dan gwagwarmayar farar hula na kasar Jean-Rémy Yama sakamakon zargin shi da rashin saka takardar haihuwar mahaifin shi 

Daga cikin wadanda aka amince da takardar takarar tasu akwai shugaban gwamnatin rikon kwaryar mulkin sojan kasar Brice Clotaire Oligui Nguema da kuma Alain-Claude Bilie By Nze tsohon Firaministan hambararren shugaban kasar Ali Bongo

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp