Wata kotu da ke zamanta a jihar Rivers ta umarci wata mata mai suna Kate Ngbor da ta daina amfani da sunan tsohon mijinta da ta rabu da shi shekaru 11 da suka gabata ba tare da bata lokaci ba.
Mai shigar da karar kuma tsohon mijin nata Cif Sam Ngbor, ya nemi kotu ta hana tsohuwar matar tasa Misis Kate Mgbor, ci gaba da bayyana sunansa a cikin sunan ta.
Kotun ta ba da umarnin cewa wacce ake kara ba ta da wani hurumi na ci gaba da anfani da sunan “Ngbor” ko “Sam-Ngbor”
Category
Labarai