Kotu a Abuja ta dakatar da Majalisar Dattawa daga ladabtar da Sanata Natasha

 

Sanata Natasha Akpoti

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da kwamitin da'a na majalisar dattawa da karbar koken jama’a daga ladabtar da sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan.

Alkalin kotun, Obiora Egwuatu, ya ba da umarnin ne a ranar Talata bayan wata takardar karar da lauyan Akpoti-Uduaghan ya shigar a gaban kotun.

A ranar 20 ga watan Fabrairun shekarar 2025, sanatar mai wakiltar Kogi ta tsakiya ta yi musayar kalamai da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, kan batun sauyin wurin zama da aka yi mata.

Kin bin umarnin shugaban majalisar Godswill Akpabio da ta yi, ya janyo cece kuce a cikin majalisar da ma wajen majalisar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp