Cocin Christ Evangelical and Life Intercessory Ministry da ke unguwar Sabon Tasha a karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna, ta raba hatsi ga mabukata sama da 1,000 domin saukaka musu azumin watan Ramadan duba da halin da kasar nan ke ciki.
Fasto Yohanna Buru, babban mai kula da cocin, ya bayyana cewa sun raba wannan tallafin ne domin karfafa zaman lafiya a tsakanin addinan biyu mazauna yankin.
Category
Labarai