Rikicin siyasa a Jihar Rivers na kara ta'azzara bayan da aka jawo shugaban jam’iyyar na jihar Tony Okocha ya bukaci Gwamna Siminalayi Fubara da ya yi murabus ko kuma majalisar dokokin jihar ta tsige shi daga mukamin sa.
Shugaban jam’iyyar ya fadi hakan ne a yayin ganawar sa da yan jarida a Fatakwal babban birnin jihar, inda ya zargi gwamnan da rashin zabuka abin a zo a gani a jihar.
Tony Okocha ya ba Fubara zabi biyu ne na yin murabus ko kuma majalisar dokokin jihar ta tsigewa.
Category
Siyasa