Shugaban komitin shirya taron muhawara na kasa ya mika wa shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar takardun kammalallen rahoton aikin da suka yi
Shugaban komitin shirya taron muhawara na kasar Nijar Dr Mamoudou Harouna Djingarey ya mika takardun rahoton kammalallen aikin da suka yi na shawarwarin da taron ya bayar ga shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar
A yayin wani kwarya kwaryan taro ne da aka gudanar a fadar shugaban kasar ta Nijar membobin komitin suka mika wannan rahoto a gaban tsoffin shugabannin kasar uku da sauran membobin gwamnatin kasar
Daga ranar 15 zuwa 20 ne dai ga watan Febarairun da ya gabata aka gudanar da taron muhawara na kasar wanda ya hada mahalarta sama da 700 daga sassa daban daban na ciki da wajen kasar wadanda suka bayar da shawarwarin na shata sabuwar al'kibilar kasar