![]() |
Nasir Idris |
Jam’iyyar APC reshen jihar Kebbi ta dakatar da mai bai wa gwamna Nasir Idris shawara kan harkokin mulki da siyasa, Kabir Sani-Giant, saboda tsoratar da mutane a da maciji a gidan gwamnatin jihar.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren jam’iyyar, Sa’idu Muhammad-Kimba, y bayyana cewa a ranar 8 ga watan Fabrairu, Kabir Sani-Giant ya shiga da maciji a gidan gwamnatin jihar, inda ya rika nunawa manyan mutane tare da basu tsoro.
Sakataren jam'iyyar Muhammad Kimba ya ce wannan abu zai iya bata sunan jam’iyyar,kuma ya saba wa kundin tsarin mulkin APC.
Dakatarwar ta shi ta fara aiki har sai an kammala gudanar da bincike da kuma yiwuwar daukar matakin ladabtarwa.