Jami’an tsaro sun yi nasarar ajalin kasurgumin dan ta'addar Lakurawa da ake kira Maigemu a jihar Kebbi

Nasir Idris

Tawagar jami’an tsaro da suka hada da ‘yan bijilanti sun yi nasarar kawar da fitaccen dan ta'addan  Lakurawa da akafi sani da  Maigemu a jihar Kebbi.

Daraktan harkokin tsaro na jihar, AbdulRahman Usman Zagga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a a Birnin Kebbi.

Ya ce an kashe Maigemu ne a ranar Alhamis a Kuncin Baba da ke karamar hukumar Arewa ta jihar Kebbi, yankin da ke fama da yan ta'addan.

Ya kara da cewa wannan ya zo ne mako guda bayan da gwamnan jihar Nasir Idris ya ziyarci al’ummar Bagiza da Rausa Kade a karamar hukumar Arewa domin jajantawa mazauna garin bisa kashe wasu mutane shida da ake zargin yan ta'addan Lakurawa ne suka yi.

A yayin ziyarar gwamnan, ya tabbatar wa al’ummomin  yankin cewa za a inganta tsaro cikin gaggawa tare da daukar matakan da suka dace don magance miyagun laifuka a yankin.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp