Hukumar Kwastam a Nijeriya, NCS, ta kama wasu kayayyakin da aka yi fasakwauri da suka kai Naira miliyan 51.9 a cikin makonni uku a yankin Adamawa da Taraba
Kwanturola mai kula da rundunar a yankin, Garba Bashir ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai ranar Laraba a Yola.
Garba ya alakanta wannan nasarar da rundunar ta samu wajen amfani da bayanan sirri da kuma hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro.
Kayayyakin da aka kama sun hada da lita 29,825 na man fetur, da aka zuba a cikin jarkoki 1,149 da tankuna hudu kowanne lita 220, wanda aka yi niyyar fitarwa ba bisa ka’ida ba.
Sai motoci uku da babur, da ake amfani da su wajen fasa kwaurin, ciki har da mota mai boye man fetur.