![]() |
Jami'an hukumar FRSC |
Hukumar kiyaye aukuwar hadurra ta FRSC ta kame motoci sama da 350 a cikin wata daya a fadin kasar, masu ɗauke da lambobin da ba a yi rejista ba.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Olusegun Ogungbemide ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a ranar Litinin a Abuja.
Kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN ya ruwaito cewa, a ranar 3 ga watan Fabrairu ne hukumar FRSC ta fara gudanar da wani samame a fadin kasar na kame motoci masu jabun lambobin da ake yi ta bayan fage.
Ya ce tun da farko an fara aikin ne a Abuja, ganin irin illar da hakan yake da shi ga tsaro, da zagon kasa ga kokarin tabbatar da doka da kuma yin illa ga tsaron kasa.