![]() |
Attahiru Bafarawa |
Wani babban hadimin tsohon gwamnan jihar Sokoto,Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya musanta batun sauya sheka zuwa jam'iyyar SDP.
Mataimakin ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da wakilin jaridar Punch a Sokoto ranar Talata.
Jaridar PUNCH Online ta ruwaito cewa a ranar Talatar da ta anyi ta yada labari a kafafen sada zumunta cewa tsohon gwamnan ya koma zuwa jam'iyyar SDP.
Idan dai za a iya tunawa, tsohon gwamnan a lokacin da yake bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP a karshen shekarar da ta gabata, ya ce ya yi hakanne domin ya fi mayar da hankali kan sauran manufofin ci gaban Arewa.