![]() |
Bola Ahmad Tinubu |
Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar kula da ilimin bai daya ta kasa UBEC, ta bayar da kudi naira biliyan 6.7 na kula da makarantar Smart School ga gwamnatin jihar Nasarawa domin magance matsalar yaran da basa zuwa makaranta a fadin kananan hukumomi 13 na jihar.
Daily Trust ta ruwaito cewa sabuwar makarantar da aka kaddamar a ranar 24 ga Mayu, 2024, an yi ta ne da nufin inganta yanayin ilimin makarantun firamare da kananan sakandare na gwamnati a fadin Nijeriya.
Babbar sakatariyar hukumar UBEC Aisha Garba ce ta bayyana hakan bayan ta duba makarantar UBEC da ke birnin Lafiya da kuma makarantar da aka gyara a karamar hukumar Akwanga a jihar Nasarawa.