![]() |
Majalisar zartarwar Nijeriya |
Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da kashe naira biliyan 507 don kammala kashi na biyu na hanyar Abuja-Kaduna-Zaria-Kano mai tsawon kilomita 164.
Ministan ayyuka, Dave Umahi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin bayan taron majalisar zartarwa wanda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta a Abuja.
Ya ce an amince da fitar da naira biliyan 733 domin shinfida tituna a sassan kasar.
Ministan ya ce majalisar zartarwar ta kuma amince da kashe naira biliyan 24 don gina Abakpa Flyover a Jihar Enugu, wanda ke iyaka da Barikin Sojoji ta 82, domin saukaka cunkoson ababen hawa a yankin.
A cewar ministan majalisar ta kuma amince da kashe biliyan 55 domin aikin hanyar Odukpani-Itu-Ikot Ekpene, wadda ta hada jihohin Cross River da Akwa Ibom.
Ministan ya kuma yi watsi da rade-radin da ake cewa gwamnatin Shugaba Tinubu na fifita Kudu kan Arewa wajen rabon ayyuka musamman hanyoyi.