Fursunoni 53,254 ke jiran shari’a Najeriya - Jaridar Punch


Wata ƙididdiga daga hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Nijeriya, ta nuna cewa kimanin fursunoni 53,254 ne ke jiran a yi musu shari’a a gidajen gyaran hali daban-daban.

Wannan na kunshe ne a cikin alkaluman da jaridar Punch ta tattara a ranar Juma’a, wadanda aka sabunta a ranar 24 ga Fabrairu, 2025. 

Kididdigar ta nuna cewa jimillar fursunonin dake tsare a Nijeriya sun kai 80,100, yayin da fursunoni 26,846 da aka riga aka yanke musu hukunci.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp