Alamu na nuna cewar wasu manyan ‘yan siyasa sun kammala shirin komawa jam’iyyar SDP biyo bayan ficewar tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai daga jam’iyyar APC mai mulki.
Shugaban jam’iyyar SDP na kasa, Shehu Musa Gabam ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, a wata tattaunawa da yayi da gidan talabijin na Trust yayin da yake mayar da martani kan sauya shekar ta El-Rufai.
Gabam ya bayyana cewa matakin da El-Rufai ya dauka ya kawo sauye-sauyen ficewa daga jihar Kaduna, inda ake sa ran wasu fitattun jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulki da sauran jam’iyyu da dama za su yi koyi da shi.
Wasu majiyoyi daga cikin jam’iyyar na nuni da cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi da tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, suma suna shirin koma jam’iyyar SDP.
El-Rufai dai ya ziyarci Aregbesola da wani malamin addinin kirista Fasto Tunde Bakare a Legas ranar Lahadi.
Ya kuma gana da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a kwanakin baya.
Wadannan ziyarce ziyarce sun kara rura wutar rade-radin cewa El-Rufai ya nuna mafarin sauye-sauyen sheka a siyasa.