Eric Challe ya halarci wasan da Kano Pillars ta doke Enugu Rangers a gasar firimiyar NPFL


Mai horar da tawagar Super Eagles ta Najeriya Eric Challe ya kalli wasan Kano Pillars da ta samu galaba akan Enugu Rangers da ci 2-1.


Wasan an fafata shi a Lahadi 02 ga Maris 2025, a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata , wasan mako na 27 a gasar firimiyar NPFL ta Najeriya.

Ana ci gaba da rade-radin cewar zuwan nasa na da nasaba da sake kiran kyaftin din tawagar ta Eagles Ahmed Musa zuwa kungiyar a wasannin ta na gaba.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp