Dalilan da suka hana mu binciken Sanata Godswill Akpabio - Majalisar Dattawa

Sanata Godswill Akphabio

Majalisar dattawan Nijeriya ta ce bata fara binciken akan zargin neman yin lalata da Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya Natasha Akpoti ke yi wa shugaban Majalisar Godswill Akpabio ba, kasancewar babu wanda ya gabatar da bukatar a hukumance.

Shugaban kwamitin yada labarai da na majalisar dattawa, Sanata Yemi Adaramodu ne ya bayyana haka a zantawar sa da gidan talabijin na ARISE, a ranar Litinin, da ya ce ba za a iya bincikar Akpabio daga majalisar dattawa ba tare da gabatar da korafi a kansa ba.

A baya Sanata Natasha ya yin wata hira da gidan talabijin na ARISE ta yi zargin cewa Akpabio ya yi mata kalaman da basu dace ba a lokacin da ta kai masa ziyara a gidansa da ke Uyo, jihar Akwa Ibom, a ranar 8 ga watan Disamba, 2023.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp