![]() |
Shugaba Bola Ahmad Tinubu |
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce duk wani mataki da ya dauka har zuwa yanzu, ciki har da batun cire tallafin man fetur ya shafi matasan Nijeriya ne da kuma makomar su.
Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin kaddamar da kwamitin tsare-tsare na taron matasa na kasa a fadar gwamnati da ke Abuja.
Ya ba da tabbacin cewa, an yi gyare-gyaren tattalin arzikin ne domin karfafa tattalin arzikin kasar don samar da wadata ga matasan Nijeriya, wadanda su ne sama da kashi 60 cikin dari na al’ummar kasar.
Ya tabbatar da cewa matasa sune fatan Nijeriya, kuma komai ya rataya a kan su, da ya ce duk shawarar da ya yanke saboda matasan ne ciki harda cire tallafin man fetur don kare makomar su.