Bayern Munich ta kammala yarjejeniya da dan wasa Joshua Kimmich domin kulla sabuwar kwantaragi

Joshua Kimmich

Bayern Munich ta kammala yarjejeniya da dan wasa Joshua Kimmich domin kulla sabuwar kwantaragi

Duk da cewa wasu kungiyoyi na nemansa, Joshua Kimmich ya nuna aniyarsa ta ci gaba da zama a kungiyar Bayern Munich.

Tun a kwanaki 10 da suka gabata ne ake ci gaba da tattaunawa tare da bangarorin da yanzu ke shirya takardu don sanya hannu nan ba da jimawa ba.

Real Madrid na daga cikin kungiyoyin da suka nuna sha'awarsu ta daukan Kimmich, sai dai tafi mayar da hankali kan Alexander-Arnold a maimakon Joshua Kimmich.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp