![]() |
Godswill Akphabio |
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya musanta zargin cin zarafi da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi masa.
Akpabio ya bayyana hakan yayin zaman majalisar a ranar Laraba, ya ce ko kadan bai taba yunkurin yin lalata da sanatan Kogi ta tsakiya ba ko wata mace ta daban.
Ya ce shi da 'yan uwansa, mahaifiyarsu ta basu cikakkiyar tarbiyya, don haka yana girmama mata sosai.
Ya kara da cewa yanzu haka yanada ‘ya’ya mata guda hudu, don haka ba zai taba cin zarafin wata mace kuma bai taba yin haka ba.