Ba mu damu da sauya shekar El-Rufai zuwa SDP ba – Jam’iyyar APC a Kaduna


Jam’iyyar APC reshen jihar Kaduna a ta bakin sakataren jam’iyyar, Yahaya Baba-Pate yace jam’iyyar ba ta damu da ficewar tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i da ya yi zuwa jam’iyyar SDP.

DCL Hausa ta ruwaito cewa Malam Nasiru El-Rufai ya fice daga jam’iyyar APC ne a ranar Litinin, zuwa jam’iyyar SDP.

Tsohon gwamnan ya bayyana rashin jituwar da ke kara ta’azzara a tsakanin kimar sa da kuma alkiblar jam’iyyar APC a halin yanzu a matsayin dalilin da ya sa ya yanke wannan shawarar.

Sakataren jam’iyyar ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Kaduna.

Ya kara da cewa jam'iyyar na da kwarin guiwa na ganin yadda take kara samun karfi a jihar, inda ya yi nuni da yadda manyan ‘yan siyasa ke kwararowar jam’iyyar a kullum.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp