Ana zargin wani magidanci da ajalin matarsa kan abincin buda-baki na azumi a jihar Bauchi


Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta damke wani magidanci mai suna Alhaji Nuru Isah mai shekaru 50 bisa zarginsa da yin amfani da sanda wajen hallaka matarsa ​​Wasila Abdullahi har lahira.

Lamarin dai ya faru ne a Fadamam Unguwar Mada dake kusa da makarantar kwalejin ’yan mata ta Gwamnati da ke jihar Bauchi.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Ahmed Wakil, yace rundunar ta some bincike kan lamarin, kuma tuni aka cafke wanda ake zargi.


 

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp