![]() |
Police |
Rundunar ‘yan sandan jihar Benuwe ta tabbatar da sakin dalibai mata uku da aka yi garkuwa da su a jami’ar koyar da aikin gona ta Joseph Sarwuan Tarka da ke Makurdi a jihar Benue.
An yi garkuwa da daliban ne a ranar 25 ga Fabrairu, 2025, yayin da suke dawowa daga wani zaman karatun dare a harabar jami’ar.
Bayan sace daliban, hukumomin jami’ar sun bayar da hutun tsakiyar zangon karatu na mako daya domin magance matsalolin tsaro.
Kungiyar dalibai ta kasa NANS da ministar harkokin mata, Imaan Sulaiman-Ibrahim, duk sun yi kira da hukumomi su kara kaimi domin ganin an maido da daliban gida lafiya.