![]() |
Kayode Egbetokun |
An yi garkuwa da wani dan sanda mai mukamin Chief Superintendent of Police wato CSP mai suna Modestus Ojiebe a kan titin Abuja zuwa Kaduna.
Wata majiya ta bayyana cewa, an kai wa babban jami’in ‘yan sandan jihar Kwara hari ne a lokacin da yake kokarin gyara motarsa da ta lalace a kusa da Barikin Dei-Dei a Abuja.
A cikin wani rahoto da mai sharhi kan al'amuran tsaro Zagazola Makama ya fitar, ya ce a lokacin da dan sandan yake kokarin gyara motar, sai wata mota kirar Mercedes-Benz tare da mutane hudu dauke da makamai suka tsaya a bayansa.
Maharan sun yi bincike tare da yi wa Ojiebe da matarsa fashin wayoyin hannu da katin cirar kudi na ATM. Sai dai da suka gano katin shaidar dan sanda ne shi, sai suka tilasta masa shiga motarsu suka tafi da shi, inda suka bar matarsa da motarsu a wurin.
Bayan faruwar lamarin,an sanar da jami'an 'yan sanda da ke Dawaki Division inda nan take aka aike da tawagar ‘yan sanda zuwa yankin.
An tsaurara bincike a wurare daban-daban na shiga da fita na babban birnin tarayya Abuja a kokarin ceto jami’in tare da cafke masu garkuwar.