An kama tsohon kwamishina a lokacin El-Rufai kwanaki kadan bayan ficewar sa daga jam'iyyar APC

Malam Nasir El - Rufa'i

Jami’an tsaro sun kama tsohon kwamishina a gwamnatin tsohon gwamna Nasir El-Rufai a Kaduna Jafaru Ibrahim Sani, ranar Alhamis.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an Operation Fushin KADA ne suka kama shi da misalin karfe 10:45 na safe, jim kadan da barin gidansa da ke cikin babban birnin jihar.

Wasu majiyoyi sun shaida wa Daily Trust cewa bayan kama shi, an kai shi kotu da ke kan titin Daura, Kaduna, kafin a tsare shi a gidan gyaran hali.

Sani dai na daya daga cikin tsofaffin kwamishinoni shida da suka fice daga jam’iyyar APC mai mulki a kwanakin baya, inda suka bi sahun mai gidan su El-Rufai wanda shi ma ya fice daga jam’iyyar.

Daily Trust ta bayyana cewa an tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, amma ba a samu jin ta bakin shi ba

El-Rufai dai ya alakanta kamun Sani da bita da kullun siyasa, ciki har da ficewarsa daga APC da kuma komawarsa jam’iyyar SDP.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp