'Yan bindiga sun bingige shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Kwara, Alhaji Idris Abubakar Sakaina.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:00 na daren ranar Asabar, da maharan suka harbe shi har lahira a kofar gidansa da ke Oke Ose a birnin Ilorin.
A cewar Jaridar Daily Trust ‘yan bindigar sun bar shi a nan cikin jini ba tare da sun dauki wani abu nasa ba.
Marigayin mai shekaru 32, an ce tsohon mataimaki na musamman ne ga shugaban karamar hukumar Moro kuma shugaban matasan Fulanin jihar Kwara.
Category
Labarai