An bindige 'Group Admin' na WhatsApp bayan ya cire wani mamba na group din


Jami'an yan sandan kasar Pakistan na tuhumar wani mutum mai suna Ashfaq da zargin hallaka wani 'Group Admin' na WhatsApp bayan ya cire shi daga group.

Rahotanni sun ce an harbe Mushtaq Ahmed da yammacin ranar Alhamis a Peshawar, babban birnin Khyber Pakhtunkhwa wanda ke kan iyaka da kasar Afganistan.

Dan uwan ​mamacinya bayyana cewa an fidda Ashfaq daga group na WhatsApp ne bayan wata sa'in sa da ta barke a cikin group din.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp