Akwai babbar maja da muke shirin yi domin kalubalantar APC – Atiku Abubakar


Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya musanta rahotannin da ake ta yadawa na ficewar sa daga jam'iyyar.

Atiku Abubakar ya ce rahotannin ficewar sa daga jam’iyyar na daga cikin kokarin da wasu ke yi na kawo rudani na hadaka da yake yi da wasu jam'iyyu.

Anga rubutu daban-daban na yawo cewa Atiku na shirin sauya sheka daga jamiyyar PDP zuwa SDP.

Sai dai ofishin yada labaran Atiku Abubakar ya jaddada cewa sabuwar majar za ta tafi da wasu jam'iyyun adawa ciki har da jam'iyyar PDP.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp