Kungiyar SERAP mai fafutikar yaƙi da cin hanci a Nijeriya ta yi kira da babbar murya ga shugaban majalisar dattawan Nijeriya Godswill Akpabio da ya gaggauta janye dakatarwar da majalissa ta yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Kungiyar ta bayyana matakin dakatarwar a matsayin rashin bin doka da kuma take ma mata 'yancin fadar albarkacin baki.
Wannan dai na a cikin wata budaddiyar wasika mai dauke da kwanan wata na 8 ga watan Maris 2025, wanda mataimakin daraktan kungiyar ta SERAP, Kolawole Oluwadare ya sa ma hannu, SERAP ta yi gargadin cewa za ta yi shari’a idan har shugaban majalisar dattawa ya ki bin gargadin cikin sa’o’i 48.
Category
Siyasa
09030463254
ReplyDelete